Mace-mace a harin bam a Mogadishu
August 5, 2018Talla
Akalla mutane 12 sun rasa rayukansu ciki kuwa har da jami'an 'yan sanda hudu yayin da wata mota makare da bama-bamai ta yi bindiga a Afgoye da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, kamar yadda hukumar 'yan sandan kasar ta sanar a ranar Lahadi. Sanarwar ta kara da cewar wasu mutane 14 da ke kusa da gurin da al'amarin ya faru na kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.
Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta Al-shaabab ta dauki nauyin wannan hari.. Kasar Somaliya dai na ci-gaba da fuskantar rashin tsaro tun daga lokacin da kungiyar Al-shabaab ta sanar da kudirinta na kau da gwamnatin kasar wacce ke da goyon bayan kasashen waje .