1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a rushewar wani gini a Lagos

Mouhamadou Awal Balarabe
May 2, 2022

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta sanar da cewa mutane takwas sun mutu sakamakon rushewar wani bene mai hawa uku a gundumar Ebute-Metta ta Lagos cibiyar tattalin arzikin kasar.

Nigeria Unglück l Rettungskräfte suchen in den Trümmern des eingestürzten Gebäudes in Ikoyi
Hoto: Benson Ibeabuchi/AFP

Ba a dai tantance musabbabin rugujewar ginin na Lagoas ba, ammai masu aikin ceto sun yi nasarar zakulo mutane 23 da suka samu munanan raunuka daga baraguzan ginin.     

Rushewar gine-gine na neman zama ruwan dare a Najeriya sakamakon tauye ka'idojin gine-gine. Ko a watan Nuwamba, sai dai rushewar wani katafaren gini da ake kan ginawa a Legas ta yi sanadiyar mutuwar mutane 45 ciki har da ma'aikatan da suke aiki a wurin. Sannan mutane uku sun gamu da ajalinsu lokacin da wani coci a rushe a watan Janairu a Fatakwal da ke yankin Neja Delta

Bincike da wani masani dan kasar Afrika ta Kudu ya gudanar ya gano gine-gine 152 da suka ruguje a Legas tun daga shekarar 2005 wato a cikin shekaru 17.