1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a shagulgulan sabuwar shekara

January 1, 2023

'Yan sanda a Yuganda sun tabbatar da mutuwar akalla mutane tara ciki har da wani yaro da shekarunsa na haihuwa ba su wuce goma ba, yayin shagulgulan murnar shiga sabuwar shekara ta 2023.

Wasan wuta ya haifar da mace-mace a birnin Kampala na YugandaHoto: Badru Katumba/AFP

Jami'an kasar Yuganda sun ce an samu asarar rayukan ne bayan da mutanen suka shaki hayakin kayan wasan wuta da ya turnike, a lokacin da aka samu turereniyar neman shiga wajen da ake wasan a Kampala babban birnin kasar. Waje ne da ke dauke da rukunin shaguna da ake kira Freedom City Mall a birnin na Kampala, daidai karfe 12 na dare agogon kasar.

Akwai dai fargabar adadin wadanda suka mutu dai ka iya zarta mutum goma da hukumomin suka sanar, saboda yawan wadanda hayakin ya hana su numfashi.