Mace-mace na karuwa a Rafah saboda luguden wuta na Isra'ila
February 9, 2024Ministocin kasashen Masar da Amurka da Qatar da Isra'ila sun yi a zama a birnin Alkahiran Masar kan yunkurin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Gaza, amma an watse ba tare da cimma biyan bukata ba. Saboda haka ne jiragen yakin Isra'ila suka karkata akalar farmakinsu zuwa yankin Rafah da ke kan iyakar Masar daGaza, duk da gargadin da kasashen
Karin bayaniGaza: Kokarin tsagaita wuta mai dogon zango:
Jiragen yakin Isra'ila sun ta yin luguden wuta tun da daren Alhamis zuwa Jumma'a a Rafah da ke zama tudun na tsira daya tilo da ya rage wa dubu dubatan Falalsdinawan Gaza. Dama samamen dakarun Isra'ila da luguden wutar sun kwashe watanni hudu suna yi a kansu ya tilasta musu fakewa da yanki na Rafah.
Karin bayani: Gaza: Za a cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta
Isra'ilana zargin cewa jagororin Hamas da take nema ruwa a jallo sun sulale daga yankin Khan Yunus na tsakiyar Zirin Gaza da yanzu take mamaye da shi.