SiyasaAsiya
Mace ta farko ta dauko hanyar zama Firaminista a Japan
October 4, 2025
Talla
Wakilai sama da dubu 900,00 suka kada kuri'a ciki har da wakilan jam'iyyar Liberal Democratic Party 295 da suka kada kuri'a ga mai ra'ayin 'yan mazan jiyan nan Sanae Takaichi, a gayaye na biyu bayan ta fafata da Shinjirō Koizumi wanda ya samu kuri'u 156.
Karin bayani:An fara takarar neman maye gurbin firaministan Japan
Takaichi na daya daga cikin makusanta kuma masu ra'ayin 'yan mazan jiya na tsohon firaministan kasar Shinzo Abe, wanda aka halaka shi a bainar jama'a a lokacin da yake wani gangami a 2022.