1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Machar ya zargi Kiir da kokarin aiwatar da mulkin kabilanci

Mouhamadou Awal Balarabe
September 12, 2025

Rikicin siyasar Sudan ta Kudu ya samo asali ne sakamakon takun saka tsakanin kabilar Nuer ta Riek Machar da kuma kabilar Dinka ta shugaban kasa Salva Kiir.

Riek Machar da Salva Kiir na fifita muradun kabilunsu a kan harkokin gwamnatin Sudan ta Kudu
Riek Machar da Salva Kiir na fifita muradun kabilunsu a kan harkokin gwamnatin Sudan ta KuduHoto: Simon Maina/AFP

'Yan adawa a kasar Sudan ta Kudu sun zargi gwamnatin Salva Kiir da yunkurin kafa tsarin mulkin kama-karya mai nasaba da kabilanci, bayan da aka zargi mataimakin shugaban kasarRiek Machar da kitsa hare-hare a Arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya kai ga tsige shi daga mukaminsa.

Jam'iyyar SPLM-IO ta Machar ta musanta laifuffukan da ake zargin mambobinta da aikatawa, ciki har da kisan kai da cin amanar kasa da kuma cin zarafin bil adama. Hasali ma, jJam'iyyar ta adawa ta ce zargin, karya ce tsagwaronta da nufin yin kafar angulu ga yarjejeniyar zaman lafiya.

Karin bayani: Fargabar rinchabewar rikicin Sudan ta Kudu

Dama dai, daurin talala da aka yi wa Riek Machar tun watan Maris ya haifar da fargabar sake faruwar yakin basasa da ya taba barkewa tsakanin 2013 zuwa 2018 a Sudan ta Kudu.

Rikicin dai ya samo asali ne sakamakon takun saka tsakanin kabilu biyu masu biyayya ga shugabannin biyu wato Nuer na Machar da kuma kabilar Dinka ta shugaban kasa Salva Kiir.