1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macky Sall ya yi ratsuwar kama aiki

April 2, 2012

Mutane kimanin 2000 ciki har da shugabannin Afirka 11 suka halarci shagulgulan ratsar da sabon shugaban na Senegal.

Senegalese opposition presidential candidate Macky Sall (R) celebrates at a news conference in Dakar March 25, 2012. Senegal's long-serving leader Abdoulaye Wade admitted defeat in the presidential election, congratulating his rival Sall, a move seen as bolstering the West African state's democratic credentials in a region fraught with political chaos. REUTERS/Joe Penney (SENEGAL - Tags: POLITICS ELECTIONS PROFILE)
Hoto: Reuters

A rantsar da sabon shugaban ƙasar Senegal Macky Sall bayan gagarumar nasarar da ya samu akan tsohon shugaba Abdoulaye Wade a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ƙarshen watan Maris.

Sabon shugaban ƙasar Senegak kenan Macky Sall ya yi rantsuwar kama aiki da cewa zai yi biyayya ga dokokin aiki a ofishin shugaban ƙasa da girmama kundin tsarin mulki, sannan ya ce zai yi amfani da dukkan ƙarfinsa don kare cibiyoyin ƙasa ƙarƙashin dokokin kundin tsarin mulki.

Ƙasashen duniya sun yaba da yadda aka samu sauyin shugabanci cikin ruwan sanyi a Senegal da cewa wani kyakkyawan misali ne ga demokraɗiyyar nahiyar Afirka. Mutane kimanin 2000 ciki har da shugabannin ƙasashen Afirka 11 suka halarci bikin ratsuwar da aka yi a wani ƙasaitaccen otel dake Dakar babban birnin ƙasar. Sall wanda ya taɓa riƙe muƙamin Firaminista ya gaji tari matsaloli da suka haɗa da yawan ɗauke wutar lantarki, marasa aikin yi da hauhawar farashin kayan abinci, sannan talakawa na saka dogon buri na ganin an samu canji.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman