Macron: A daina harba bama-bamai a Ukraine
February 18, 2022A lokacin da yake tsokaci a birnin bruxelles, Macron ya nuna damuwa dangane da harbe-harben bama-bamai da aka samu a gabashin Ukraine, tare da nema a koma kan teburin tattaunawa domin magance takaddamar Rasha da Ukraine. A nasa bangaren shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya nanata bukatar samar da matakai biyu da suka kunshi takunkumi idan sojojin Rasha suka kai hari da kuma kokarin samar da maslahar diflomasiyya.
Tashin hankali ya yi kamari a wannan Jumma'a a gabashin Ukraine, inda 'yan aware masu goyon bayan Rasha suka ba da umarnin a kwashe fararen hula zuwa Rasha, yayin da Amirka ta yi Allah wadai da abin da ta kira tsokana ta Rasha don neman damar afka wa ukraine da fada. ‘Yan sa'o'i masu zuwa ne za a samar da hadin kai tsakanin Turai da Amirka, a wani taron bidiyo tsakanin shugaban Amirka Joe Biden da shugabannin Turai da dama.