Faransa na neman hadin kai a Mali
May 31, 2021Talla
Da yake magana a taronsa na karshe da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke shirin barin gado a watan Satumba, Macron ya ce Faransa za ta sa ido sosai a Mali don ganin kasar ta koma tafarkin dimukuradiyya bayan juyin mulki na biyu cikin watanni Tara.
Faransa ta kuma gargadi sojojin da suka saka yi juyin mulki na biyu a Malin cewa, wajibi su mutunta lokacin da aka tsara na sake gudanar da zabe a 2022. Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan da kungiyar ECOWAS ta dakatar da kasar Mali yayin wani taron gaggawa a kasar Ghana.