Macron ya soki kwamitin sulhun MDD
November 16, 2020Talla
Yayin wata hira da jaridar Grand Continen a birnin Paris, Shugaba Macron ya ce lokaci ya yi da kasashen nahiyar Turai za su kare 'yancinsu. Faransa na cikin kasashe biyar masu kujerar din-din-din a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kowace ke da ikon hanawa ko tabbatar da kudiri.
Amirka na amfani da ikonta wajen kare martabar Isra'ila, yayin da Rasha ke tsayuwar daka na hana kwamitin kakabawa kasar Siriya takunkumi. A baya dai kalaman Macron na ayyana kungiyar tsaro ta NATO da mushen Gizaka ya tada kura.