1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban kasar Faransa yayi kira ga Saudiyya

Zulaiha Abubakar
November 30, 2018

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya shaidawa Yarima Muhammad bin Salman cewar kasashen Turai za su bukaci masana tsaro su binciki kisan 'dan jarida Jamal Kashoggi bayan bukatar kawo karshen yakin Yemen.

Argentinien G20 Gipfel - Macron und bin Salman
Hoto: Getty Images/AFP/B. Al-Jaloud

Emmanuel Macron yayi wannan kira ne a yayin da shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya G20 ke gudanar da babban taronsu a kasar Ajentina a wannan Juma'ar.

Daga cikin shugabannin da suka halarci taron akwai wadanda suka soki lamirin matsayin Amirka kan zargin da ake wa kasar Saudiyya game da kisa da kuma batar da gawar 'dan Jarida Kashoggi.