Macron ya karbi bakoncin Putin a fadar Versaille
May 29, 2017Sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron a wannan Litinin ya karbi bakoncin shugaban Rasha Vladimir Putin a fadar Versaille mai dadadden tarihi da ke a wajen birnin Paris, a wani abinda ke zama bude sabon babi na huldar dangantaku tsakanin kasashen biyu.
Macron ya yi alkawarin yin tattaunawa mai zafi a taronsa na farko da shugaban Rasha biyo bayan yakin neman zabe da tawagar Macron din ta zargi kafafan yada labarun Rasha da kokarin yi wa harkokin demokradiyyar Faransa kutse.
Macron wanda ya karbi ragamar shugabancin Faransa makonni biyu da suka gabata, ya ce tattaunawa da Rasha tana da muhimmanci wajen tinkarar jerin batutuwa da duniya ke takaddama kai. Duk da haka dangantakarsu na cike da rashin yarda inda gwamnatocin Paris da Mosko ke goyon bayan bangarori mabanbanta a yakin basasar kasar Siriya, kana suna kai ruwa rana kan rikicin Ukraine.