Taron kolin Afirka da Faransa a Kenya
May 6, 2026
Talla
Shugaban zai kai ziyara ne saboda taron kolin Afirka da Faransa da za a yi, a Kenya, karo na farko da za a yi shi a ƙasar da ke amfani da Turancin Ingilishi, tare da mai da hankali sosai kan zuba jari a fannin tattalin arziki.
Taron koli na birnin Nairobi, wanda aka yi wa lakabi da"Africa Forward"a Turance, zai zama na farko a ƙarƙashin jagorancin shugaban Faransa da zai haɗa sauran shugabannin ƙasashe da gwamnatocin tun lokacin da ya hau mulki a shekarar ta 2017.
Kafin ya isa Kenya, Macron zai tsaya a Masar a ranar Asabar, inda shi da takwaransa Abdel Fattah al-Sisi za su bude Jami'ar Senghor Francophone a birnin Alexandria.