Madugun adawa ya zama Firaminista a Chadi
October 13, 2022Daga hamshakin mai adawa da manufofin gwamnatin marigayi Idriss Déby, Saleh Kebzabo ya sauya matsayi zuwa mukamin sabon firaminitan gwamnatin hadin kan kasa da dan abokin hamayyarsa Idriss Deby ya kafa wato Mahamat Idriss Déby.
Nadin tsohon jagoran na 'yan adawa na zuwa bayan marabus din firaministan gwamnatin rikon kwarya Albert Pahimi Padacké ya yi daga mukamin.
Wasu masu sharhi kan al'amurran siyasa a Chadi na cewa nadin Saleh Kebzabo a mukamin firaminitan bai zo masu da mamaki ba, duba da irin dangantakar da ta kasance ko da yaushe da gwamnatin marigayi Idriss Déby Itno.
'Yan kasar Chadi da dama na tuni da rashin goyon bayan da ya nuna wa dan takarar jam'iyyun adawa janar Abdelkader Kamougué, da ya samu nasarar kai wa matsayi na biyu a yayin zaben shugabancin kasa a 1996.
Da wannan irin wannan takon siyasa Saleh Kebzabo ya sha tafiyar da harkokinsa na yau da kullum ko a wannan karo, Bedoumra Kordjé tsohon kusa a gwamnatin Deby kuma daya daga cikin masu fafutikar ganin taron kolin da ya shata alkiblar kasar ya yi gagrumar nasara.
Ko baya ga suka da caccakar da masu barra'i da babban taron kolin kasar kan matakin nada sabuwar gwamnati, wasu daga cikin masu adawa da gwamnatin Mahamat Idriss Déby na ganin cewar nadin Saleh Kebzabo a mukamin na firaministan ba shi da wani tasiri.
Mahamat Zen Cherif shugaban wata jam'iyyar adawa ne a kasar na cikin masu wannan ra'ayi.
Sai dai shi kuwa Jean-Bernard Padaré, kakakin jam'iyyar MPS da ta yi mulkin Chadin, jinjina ya yi da dora Kebzabo a mukamin yana mai bayyana shi a a matsayin wani ci gaba.
Tun bayan nada sabon firaminitan a jiya ra'ayoyi mabanbanta suka karade daukacin kasar da ma a shafukan sada zumunta na zamani, inda wasu har gobe ya barsu cike da mamaki.