1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Gwamnati ta saki Hama Amadou

Salissou Boukari LMJ
March 31, 2020

A Jamhuriyar Nijar magoya bayan jam'iyyar adawa ta Lumana Afirka da sauran 'yan adawa sun nuna farincikinsu dangane da sakin da gwamnati ta yi wa madugun 'yan adawar kasar Hama Amadou.

Hama Amadou nigrischer Oppositionspolitiker
Madugun adawar Jamhuriyar Nijar Hama AmadouHoto: DW/S. Boukari

Sakin na Madugun 'ya adawar ta Nijar Hama Amadou dai ya tabbata ne, bayan da aka ji sunansa daga cikin jerin sunayen mutane 1,540 da aka sanar ta gidan radiyon kasar wadanda Shugaban Issoufou Mahamadou ya yi wa afuwa. Sai dai wannan dan kason da aka sallamo ya sha banbam da sauran, domin kuwa shi ne Madugu 'yan adawa na Nijar. Ganin cewa sakin na Hama Amadou ya zo ne a lokacin da ake fama da annobar cutar Coronavirus, madugun adawar ya yi kira ga al'ummar kasar ta Nijar da su bi dokokin kare kansu daga kamuwa da cutar. 

Ofishin jam'iyyar adawa ta Lumana Afrika a Jamhuriyar NijarHoto: DW/D. Köpp

Abin jira dai a gani shi ne ko wanne mataki Hama Amadou da jam'iyyarsa za su dauka a nan gaba, ganin cewa a yanzu ya dawo cikin iyalinsa kuma babu wata tuhuma a kan shi, ko da yake a baya an yi batun cewa daurin da aka yi ma sa na tsawon shekara guda a dokance tamkar ya rasa wasu 'yanci ne da yake da su na dan kasa na yin zabe ko kuma na a zabe shi. 
 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani