Maduro ya musanta laifin da ake tuhumarsa
January 5, 2026
Maduro mai shekaru 63, wanda ya fara gurfana a gaban wata kotun tarayya a Manhathan da ke birnin New York, kwana guda bayan kama shi daga kasarsa zuwa Amurka, ya ce "Ba ni da laifi, kuma niu mutumin kirki ne"
Ya kara tabbatar wa kotu cewa yana Allah wadai da kutsen da sojoin Amurka suka yi a kasarsa a lokacin da suka kama shi da matarsa.
Ita ma matar Maduro Cilia Flores, ta musanta aikata laifin da ake tuhumarta. Kotun ta dage shari'ar zuwa 17 ga watan Maris.
Tun da farko ana zargin Maduro da sa ido kan cibiyoyin safarar hodar iblis da ke hada kai da kungiyoyin ta'adda a kasar Mexico kamar Sinaloa da Zetas da kuma 'yan tawayen FARC na kasar Colombia da gungun kungiyoyin ta da zaune tsaye a Venezuela kamar Tren de Aragua.
Maduro ya dade yana musanta zargin, yana mai cewa bita da kullin siyasa ce kawai don mamaye kasar mai arzikin man fetur. Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tafka muhawara kan illolin harin da Amurka ta kai Venezuela yayin da Rasha da China suka yi Allah wadai da matakin.