1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Norway za ta sasanta rikicin Venezuela

Abdul-raheem Hassan
July 8, 2019

Wakilan gwamnatin Venezuela da bangaren adawa za su gana a tsibirin Barbados domin fara tattauna batun kawo karshen rikicin siyasar kasar da ya ki ci yaki cinyewa.

Bildkombo Venezuela Guaido Maduro

Kasar Venezuela ta jima tana fama da rikicin shugabancin tun bayan da jagoran adawa Juan Guaido ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa a farkon shekarar 2019, matakin da Shugaba Maduro ke ganin rashin mutunta tsarin dimukuradiyya ne.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 66 ne suka mutu a kasar sakamakon zanga-zanga a watannin biyar na farkon shekarar 2019, yayin da wani sabon rahoto ya bankado yadda jami'an tsaron gwamnati suka kashe mutane sama da 6,000 da gangan.