Mafita ga rikicin kuɗin Girka
August 23, 2012Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta buƙaci hukumomin Girka da su ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziƙin su, kamar yanda suka cimma a yarjejeniyar da suka ƙulla tare da ɓangarorin da suka ba su tallafin farfaɗo da tattalin arziƙin su. Merkel ta furta hakan ne jim-kaɗan gabannin ganawar ta da shugaban Faransa Francoir Hollande a birnin Berlin, fadar gwamnatin Jamus.
Ta kuma ce yana da muhimmanci a dakata a jira rahoton da masu bincike daga tarayyar Turai da asusun bayar da lamuni a duniya na IMF da kuma bankin Turai za su gabatar game da ci gaban da aka samu ko kuma akasin haka a shirye-shiryen tsuke bakin aljihun da hukumomin na Girka ke aiwatarwa ya zuwa yanzu, domin tantance ko ya dace ta ci gaba da zama a cikin gamayyar ƙasashen Turai da ke yin amfani da takardar kuɗin Euro ko kuma a'a.
A na shi ɓangaren, shugaba Hollande na Faransa cewa yayi yana goyon bayan Girka ta ci gaba da kasancewa cikin gamayyar ƙasashen Turai 17 da ke yin amfani da takardar kudin Euro, amma kuma zaɓi ya ragewa su 'yan Girkan ne, ko da shike kuma ya ce akwai bukatar Girka ta yi namijin ƙoƙari wajen cimma burin fafado da tattalin arziƙin ta.
A dai wannan Jumma'ar ce firay ministan Girka Antonis samaras zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, kana ya gana da shugaban Faransa Francoir Hollande ranar asabar a birnin.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu