Neman maslaha kan zanga-zanga a Paris
December 3, 2018Emmanuel Macron na kokari domin magance sake aukuwar zanga zangar da ta gudana a birnin Paris a kwanakin baya game da karin haraji kan man fetur wadda ta rikide zuwa mummunar tarzoma.
A halin da ake ciki dai gwamnatin ta ce ba ta da niyyar kafa dokar ta baci a matakin dakile zanga zangar ta masu sanye da taguwar da aka yiwa lakabi da yellow vest.
Shugaban ya bukaci ministan cikin gida Christophe Castaner ya shirya yadda jami'an tsaro za su tunkari matsalar da yi wa tubkar hanci. Yayin da a nasa bangaren Firaminista Edouard Philippe zai tattauna da shugabannin jam'iyyun siyasa da wakilan masu zanga zangar. Bayan ganawar firaministan zai sanar da matakan da za a dauka domin magance bukatun masu zanga zangar sannan majalisar dokoki ita ma za ta yi muhawara kan batun a ranakun Laraba da Alhamis.
Jigon bukatun 'yan zanga zangar shi ne shugaba Macron ya soke karin harajin da ya yi kan man fetur da man diesel wanda zai fara aiki daga watan Janairu mai kamawa. Kasancewar masu zanga-zangar ba su da shugabanni na kasa da kuma sabanin da ake da su kan wasu bukatun nasu, ya sa zaman tattaunawa da su cikin wata sarkakakiya, ko da yake galibi suna korafi ne kan tsadar rayuwa.