China ta fadi sirrin maganin Corona
April 9, 2020![China Wuhan provisorisches Krankenhaus für Coronavirus-Patienten](https://static.dw.com/image/52292270_800.webp)
Talla
Likitocin sun ce tun a watan Janairun da ya gabata suke amfani da maganin mai suna Kaletra. Jagoran likitocin mai suna Zhang Dingyu ya ce a cikin kwana biyu zuwa uku da suka fara bayar da maganin HIV din ga masu Corona, sun ga hunhunsu ya sauya kuma sun fara samun sauki.
Sai dai a watan da ya gabata wani bincike ya ce maganin HIV ba ya iya aiki a kan cutar Corona, to amma jagoran likitocin na Wuhan ya hakikance cewa su sun jarraba maganin HIV kuma ya musu aiki.