1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Magoya bayan soja sun yi zanga-zanga a Sudan

February 5, 2022

A wani abu da ke kara fito da rarrabuwar kawuna a Sudan, bangaren da ke goyon bayan sojojin sun sake fitowa a wannan Asabar, inda suke nuna amincinsu ga Janar Al- Burhan.

Sudan
Hoto: Marwan Ali/AP/picture alliance

Dubban magoya bayan soja a Sudan, sun sake yin wani gangami a gaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke a Khartoum babban birnin kasar, watanni bayan zanga-zangar nuna adawa da juyin mulki.

Wannan dai na ci gaba da nuna yadda kawuna suka rarraba a siyasar Sudan din, kasar da ke cikin jerin kasashen masu raunin tattalin arziki a duniya.

Wasu daga ciki magoya bayan sojin na Sudan a bisa rakuma, na kalamai ne da ke tir da sa bakin kasashen duniya cikin al'amuran kasar, suna mai da yaba wa sojojin kasar.

Suna dai jaddada goyon bayansu ne a gaban ofishin na MDD, ga jagorancin Janar Abdul Fattah al-Burhan.

Daruruwan 'yan kasar daga wasu sassa ma dai sun isa birnin na Khartoum domin damawa cikin wannan gangamin.