Mahaifiyar El-Rufai ta rasu
March 27, 2026
Mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya Hajiya Umma El-Rufai ta rasu daidai lokacin da hukumomin Najeriya ke ci gaba da tsare dan nata Malam Nasir Ahmad El-Rufai bisa zarge-zargen cin hanci.
Rahotanni sun ce Hajiya Umma ta rasu tana da kimanin shekaru 93, kuma ta rasu ne a wannan Juma'a a kasar Masar.
Karin bayani: El-Rufai zai ci gaba da zama a hannun hukuma
Tuni dai mutane da dama, ciki har da abokai da na kusa da iyalin El-Rufai, suka fara mika sakonnin ta'aziyya tare da addu'o'i ga marigayiyar. Daga cikin masu jimamin wannan rashi akwai tsohuwar kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Mohammed Baba, wadda ta bayyana kaduwarta kan samun labarin.
Kawo yanzu dai iyalan El-Rufai ba su bayyana wuri da lokacin da za a yi jana'izar mamaciyar ba.