1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yadda aka hau arfa

Abdul-raheem Hassan
June 27, 2023

Akalla musulmai miliyan biyu da rabi daga sassan duniya sun gudanar da hawan Arfa a cikin yanayi na tsananin zafi a birnin Makka. Wannan shi ne karon farko da aka samu yawan mahajjata tun bayan annobar corona.

Mahajja a Makka
Hoto: Amr Nabil/AP/picture alliance

Daruruwan mutane sun yi cicirindon hawa dutsen Arfa wurin da Annabi Muahmmad tsira da aminci su tabbata a gare shi ya yi huduban karshe. Hawan Arfa na a matsayin kololuwar aikin hajji ga alhazai.

Hajjin shekarar 2023, ya shiga tarihi saboda shi ne karon farko da aka samu yawan alhazai fiye da miliyan biyu da rabi. Sai dai maniyyata na aikin hajjin a cikin yanayi na tsananin zafi har maki 46 a ma'aunin celcius a kasar Saudiyya.