1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahamud Abbas ya ziyarci zirin Gaza.

May 22, 2007

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya ziyarci zirin Gaza, a yunƙurin dakatar da hare-haren da yankin ke fuskantan daga Isra´ila, da kuma ɗorewar yarjejniyar tsagaita wutar da a ka cimma, tsakanin Hamas da Fatah.

Saidai saukar sa zirin ke da wuya, wasu jiragen sama masu durra angula na Isra´ila su yi amen wuta a kudancin Gaza, tare da jima mutane 4, mummunan raunuka.

Ranar 16 ga watan da mu ke ciki, Isra´la, ta ƙaddamar da wani gagaramin hari a Gaza, wanda ya zuwa yanzu, ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 40.

Sannan a game da rikici tsakanin Hamas da Fatah, mutane fiye da 50 su ka kwanta dama, kamin cimma yarjejeniyar sulhu, a makon da ya gabata.

Mahamud Abbas, da Praministan Isma´ila Hanniey, za su gana nan gaba domin tantanawa a kann hanyoyin ƙarfafa zaman lahia a zirin Gaza, da ma Palestinu baki ɗaya.