1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan bindiga sun kashe manoma a jihar Kaduna

Abdul-raheem Hassan
July 6, 2026

Akalla manoma tara sun sun mutu yayin da aka yi garkuwa da wasu da dama a wani hari da 'yan bindiga suka kai kauyen Kakangi da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Wani jami'in sojan Najeriya a fagen daga a garin Bama
Wani jami'in sojan Najeriya a fagen daga a garin BamaHoto: STEFAN HEUNIS/AFP

Maharan sun kai farmakin ne ranar Asabar, inda suka afkawa manoman da ke aiki a gonakinsu sannan suka bude musu wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum tara daga bisani suka yi awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba kawo yanzu.

Wani rahoton tsaro da aka shirya wa Majalisar Dinkin Duniya ya ce harin na daga cikin jerin hare-haren da kungiyoyin 'yan bindiga ke kara kai wa manoman karkara a arewaci da tsakiyar Najeriya a lokacin damina. Rahoton ya nuna cewa maharan na kai hare-hare musamman kan kauyukan da suka bijirewa umarnin 'yan bindiga na biyan harajin da suke tilastawa mazauna yankunan.

Kabiru Ishaq, wani shugaban al’umma daga Birnin Gwari, wanda ya ziyarci kauyen domin jajantawa, ya bayyana cewa an kashe mutane 10. Ya ce harin na ramuwar gayya ne biyo bayan kashe wani dan bindiga da manoma suka yi a wani yunkurin fashi da bai yi nasara ba a ranar, kuma rahoton ya tabbatar da hakan a matsayin musabbabin harin.

Jihar Kaduna na ci gaba da kasancewa cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren 'yan bindiga, musamman a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Chikun da kuma Kajuru. Masana na gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare kan manoma a lokacin damina na iya shafar noma, tare da kara barazana ga wadatar abinci da tsaron rayuka a yankin.