1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahara sun kashe mutane da dama a Kwango

August 8, 2026

Rahotanni daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango na cewa, wasu mahara da ke da alaka da IS sun kashe mutane 13 a kauyen Banana Ecole da ke kusa da iyakar kasar da Yuganda.

Mahara sun kashe mutane da dama a Kwango
Mahara sun kashe mutane da dama a KwangoHoto: Zanem Nety Zaidi/Xinhua/IMAGO

Maharan sun kuma yi wa mutanen garin fashi tare da kona musu gidajensu. Shugaban kungiyar farar hula ta birnin Mambasa, Marie-Noelle Anotane ta zargi kungiyar ADF da alhakin kai harin, inda ta ce maharan sun yi amfani da dabarun irin na kungiyar ne.

Karin bayani: Harin ta'addanci ya kashe mutanen Jamhuriyar Kwango kusan 20

Harin ya tilastawa mutane daukar zabi daya, zama a cikin fargaba a garin ko kuma kaura zuwa yankunan da cutar Ebola ke yaduwa a kasar. Kungiyar ADF, wadda ta samo asali daga Uganda kuma ta yi mubaya'a ga kungiyar IS a shekarar 2019, ta dade tana gudanar da ayyukanta a kan iyakar. Kana tana daya daga cikin kungiyoyi da dama da ke aiki a Kwango, inda suke yawan kai hare-hare kan fararen hula. A watan Yulin 2025, kungiyar ta kashe mutane 66 a gabashin kasar, harin da Majalisar Dinkin Duniya ta kwatanta da kisan kiyashi.