1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Guguwar iska ta tafka barna a Amurka

Ramatu Garba Baba
March 25, 2023

Mutum akalla 23 aka tabbatar sun mutu a sakamakon wata mahaukaciyar guguwa da ta tafka barna a jihohin Mississippi da Alabama da ke kudancin Amurka.

Mississippi da Alabama sun fuskanci munmunar guguwar iska
Mississippi da Alabama sun fuskanci munmunar guguwar iskaHoto: AFP/The City of Monroe

Wata mahaukaciyar guguwar iska mai tafe da ruwan sama mai karfin gaske ce, ta lakume rayuka akalla ashirin da uku tare da lalata tarin gine-gine da katse hanyoyin wutar lantarki, a jihohin Mississippi da Alabama da ke kudancin Amurka.

Yanayin munin lamarin ya sa, hukumomi sun gargadi jama'a da su yi taka tsan-tsan a yayin da suke cewa, har yanzu akwai kalubalen da ake fuskanta mai barazana ga rayuwar al'umma a yankunan. Iftila'in ya tafka barna da kawo yanzu ba a iya tantance asarar da aka tafka daga guguwar iskar ta daren ranar Jumma'ar da ta gabata ba.