Mahawara kan 'yan sandan jihohi
July 13, 2018Gazawa ko raguwar tasirin da jami’an ‘yan sandan da ake da su a Najeriyar ne dai ya fara dago wannan batu na bukatar samar da ‘yan sanda na jihohin, lamarin da ya kai ga matsin lamba biyo bayan yawaitar munanan kasha-kashen da ake fuskanta a kasar. Alamu na a zahiri lalacewar rashin tsaro da ta kai ga babu birni ba kauye, kisan jama’a da sace su ne kawai ake yi ba tare da hukunta masu laifi ba.
Majalisar da ta ba da kai bori ya hau a kan wannan batu, ta kai ga gabatar da kuduri a karkashin mataimakin shugaban majalisar Sanata Ike Ekweremadu da ya bayyana fata ta kai wa ga amincewa da kuduri. To sai dai tun kafin a yi nisa da alamun ra’ayoyin ‘yan majalisar ya sha bamban a kan wannan batu, doming a Sanata Kabiru Marafa daga jihar Zamfara, inda ake fama da kashe-kashe ya ce akwai fa gayra a batun.
Za’a sa ido a ga irin fafatawar da za’a yi a kan wannan kuduri da a fili wani bangaren Najeriyar ke kan gaba wajen dage wa a samar da shi, a yanayin da ake fama da yadda za’a yi da jami’an sa kai na ‘yan banga irin na Peace Corp da shugaba Buhari ya ki sanya hannu a dokar halarta su.