1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawarar Bundestag akan Libiya

February 24, 2011

Tashe-tashen hankula sai daɗa yin tsamari suke yi a ƙasar Libiya, kuma duk da rahotanni masu rikitaswar da ake samu, amma akwai tabbacin cewar yawan rayukan da suka salwanta sun durfafi dubbanni.

Zaman taron majalisar dokoki ta BundestagHoto: AP

A zaman mahawarar da tayi majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta duba halin da ake ciki a ƙasar ta Libiya inda kuma dukkan wakilan majalisar suka nuna kaɗiuwarsu da ci gaban da ake samu a ƙasar. Jami'an siyasar dai na sha'awar ɗaukar wani sahihin mataki bisa manufa ta la'akari da irin ɗanyyen aikin dake faruwa a Libiya da kuma munanan matakai da sojoji masu biyayya ga Gaddafi ke ɗauka. Tazara tsakanin Berlin da Tripoli bata zarce kilomita dubu biyu ba, kuma ƙasar ta arewacin Afirka tana maƙobtaka da Turai. Amma ana fama da tafiyar hawainiya daga ɓangaren Turai. Ƙasashen na hiyar sun yi barazanar ɗaukar matakai na takunkumi, amma ƙasar Italiya na hana ruwa gudu. An lura da rashin haƙuri a zukatan wakilan majalisar dokokin Jamus ta Bundestag lokacin mahawararsu akan Libiya. An ma fi lura da hakan ne daga wakilin jam'iyyar the Greens Hans-Christian Ströbele, ƙwararren masani akan manufofin ƙetare:

Wakilin jam'iyyar The Greens Hans-Christian StröbeleHoto: AP

"Abin dake faruwa ba abin jurewa ba ne kuma wajibi ne kafofi na ƙasa da ƙasa kama daga Majalisar Ɗinkin Duniya zuwa ga Ƙungiyar Tarayyar Turai su fito fili su ƙalubalanci kashe-kashen gillar dake faruwa su kuma ɗauki matakin da ya dace bisa manufa ko da kuwa zai haɗa ne da ƙaƙaba takunkumi."

Jiragen ruwan yaƙin Jamus zasu jingina a gaɓar Libiya

Tuni dai sojan ruwan Jamus suka tura jiragen ruwan yaƙi zuwa gaɓar tekun Libiya domin taimakawa wajen kwashe Jamusawa daga ƙasar idan zarafi ya kama. Ströbele na fatan ganin waɗannan jiragen sun kuma taimaka wajen kai kayan taimako ga mabuƙata. Gwamnatin haɗin guiwa ta Christian Union da Free Democrats dai a wannan karon bata yi wata-wata ba wajen bayyana matsayinta dangane da halin da ake ciki a Libiya, bisa saɓanin yadda lamarin ya kasance dangane da Tunesiya da Masar kwannan baya. To sai dai kuma hakan ba ya nufin ɗaukar wani ƙwaƙƙwaran mataki bisa manufa. Wakilin 'yan Christian Union a majalisar dokoki Andreas Schockenhoff yayi kira ga gwamnati da tayi amfani da tasirin da take da shi a Majalisar Ɗinkin Duniya inda ya ce:

Andreas Schockenhoff wakilin 'yan Christian Union a BundestagHoto: DW

"Wajibi ne kwamitin sulhu ya tattauna akan matakan da za a ɗauka don kare al'umar Libiya daga sojojin hayan dake rufa wa gwamnatin Gaddafi. Muna sa ran ganin Jamus da sauran ƙasashen Turai sun gabatar da matakin farko domin kiran zaman gangami na kwamitin sulhun. Ana iya zatar da ƙudurin hana zirga-zirgar jiragen sama zuwa Libiya domin hana kwararar sojojin hayan zuwa ƙasar."

Taron ministocin cikin gida na Turai bai cimma matsaya ba


To sai dai kuma ba dukkan wakilan majalisar dokokin ta Bundestag ne ke goyan bayan irin wannan kira ba, inda wasu daga cikin wakilan ke ganin gabatar da irin wannan mataki zai ƙara iza ƙeyar Gaddafi wajen ƙara gallaza wa al'umar Libiya. A kuma tattaunawar da ministocin cikin gida na ƙasashen Turai ke gudanarwa a Brussels ba a cimma wata daidaituwa ba a game da yadda zasu tinkari matsalar tuttuɗowar 'yan gudun hijira daga arewacin Afirka zuwa ƙasashen na Turai, musamman dangane da ɗariɗari da sauran ƙasashen ƙungiyar ke yi game da karɓar 'yan gudun hijirar domin rage wa ƙasar Italiya raɗaɗin da take fama da shi game da dubban dubatar 'yan gudun hijirar dake ya da zango a cikinta.

Mawallafi: Christoph Hasselbach/Ahmad Tijani Lawal

Edita: Shehu Usman Shehu