1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Mahukunta na neman yafiyar bashi

September 25, 2024

Ya zuwa watan Maris na shekarar bana, bashin da yake kan Najeriyar ya sake hawa zuwa dalar Amurka miliyan dubu 86 ko kuma Naira Triliyan 125 a kasar da ta kalli yafiya kan bashin kasa da shekaru 20 da suka gabata.

Najeriya | Bashi |  Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed TinubuHoto: Sodiq Adelakun/AFP

Daga dukkan alamu batun karuwar bashin a kan Najeriya da shekaru 20 din suka gabata aka daga mata kafa ta hanyar yafe mata dimbin basussuka, ya janyo damuwa tsakanin 'yan mulkin kasar da ke neman gaza kai wa ya zuwa sauke nauyi. Najeriyar dai, na shirin ta koma kan tsohon karatun da a karkashinsa kasar ta samu yafiyar bashin. Wani sabon kamfen din kasar cikin zauren Majalisar Dinkin Duniya, na neman a sake yafe bashin da ake bin Najeriya da ma ragowar matalautan kasashe. Ba tare da yafiya kan bashin ba, akwai wahala Najeriyar a tunanin mahukuntan da ma ragowar kasashe matalauta su cimma ci-gaban tattalin arzikin al'ummarsu. To sai dai kuma duk da dauri irin na deman minti da batun bashin ke yi ga kasashe kamar Najeriyar, zai yi wuya  a sake yafe bashin a tunanin Farfesa Kamilu Sani Fagge da ke zaman kwarrare a kan batun mulki da kokarin raya kasa.

Kano: Neman mafita ga tsadar man fetur

03:06

This browser does not support the video element.

A shekara ta 2006 ne dai Najeriyar ta biya dalar Amurka miliyan dubu 12 aka kuma yafe mata wasu dubu 18. a cikin wani tsarin da ke zaman yafiya ta farkon fari ga Najeriyar. To sai dai kuma sabon kamfen din da ke zuwa a lokacin da masu mulkin kasar ke aiwatar da jerin bukatun cibiyoyin bashin na duniya, na zaman alamu na rashin gaskiya a bangare na hukumomin kudi na duniya da su kansu masu mulkin kasar a fadar Dakta Isa Abdullahi da ke zaman masanin tattali na arziki a Najeriyar. Sama da Naira triliyan 20 ne dai ko kuma daya a cikin shida na daukacin basukan kasar ne sabuwar gwamnatin kasar ta karbo a cikin shekara daya da rabi, bashin kuma da ya kasa fitar da daukacin kasar cikin halin rudu na tattalin arzikin da ke dada nisa a halin yanzu.