1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kocin tawagar kwallon kafar Kamaru ya yi barazanar murabus

October 12, 2024

Marc Brys na takun saka da hukumar kwallon kafar Kamaru saboda rashin jituwa tsakaninta da ma'aikatar wasannin motsa jiki ta kasar kan tsarin nada mataimakan mai horaswa.

Kocin Kamaru ya yi barazanar murabus
Kocin Kamaru ya yi barazanar murabusHoto: KURT DESPLENTER/picture alliance

Mai horas da tawagar 'yan wasan kwallon kafar Kamaru ta 'Lions Indomptables' Marc Brys ya yi barazanar yin murabus bayan wani sabon al'amari da ya auku a ranar Asabar a lokacin da kasar ta doke Kenya da ci hudu da daya (4-1) a fafatawar da suka yi a wasan neman gurbin buga gasar AFCON ta 2025 da za a yi a Moroko.

Karin bayani: FIFA ta haramta wa Samuel Eto'o shi wasanni

Mai horaswar dan asalin kasar Beljiyam ya ce ya fusata sosai da kutsen da hukumar kwallon kafa ta Fecafoot karkashin Samuel Eto'o ta yi masa na cire sunan matakinsa Joachim Mununga daga jerin wadanda za su tafiyar da wasan a hukumance.

Har ila yau Marc Brys ya ce idan haka ta sake faruwa to ba makawa zai yi bankwana da aikin haros da tawagar da ya fara jan rangama a watan Afrilun da ya gabata bayan ya gaji Rigobert Song.