Nijar: Mahukunta na kamen magungunan jabu
September 18, 2025
Haka nan ma hukumomin birnin na Yamai fadar gwamnatin Jamhuriyar Nijar, sun yi nasarar kwace tarin kayan maye da magungunan jabu a kasuwannin magunguna na bayan fage da kuma wuraren shakatawa da ma gidajen badala. Sai dai kuma wasu 'yan kasuwar sun nuna damuwarsu, dangane da yadda aikin kamen kayan abincin a shgunan nasu ke gudana.
Shin wannan sabon abu ne a Jamhuriyar Nijar?
Wannan dai shi ne karo na uku a cikin wannan shekara ta 2025 da mahukuntan ke kaddamar da samame a kasuwanni da shaguna da kuma wuraren shakatawa na birnin Yamai, domin kama kayan abincin da suka tashi aiki da magungunan jabu da kuma kayan maye da kuma kwalaben shisha da sauran kayan hada ta a wuraren shakatawar matasa.
Gwamnan birnin Yamai Janar Abdou Assoumane ya yi karin bayani kan kayayyakin da suka kama a wannan karo. "Mun kama ton 30 da kilogram 200 na kayan abinci a kasuwanni da shaguna......."
Hukunci ga masu sayar da irin wdannan kaya
Da yake tsokaci a wajen kone wadannan kayayyaki, mukaddashin babban mai shigar da kara na birnin Yamai Malam Alichina Kourgueni Amadou ya ce, daga yanzu duk mutanen da za a samu da aikata laifin sayar da kayan abincin da suka tashi aiki ko ungunan jabu da kayan shishar za su hadu da fushin hukuma.
To sai dai wasu 'yan kasuwar na ganin, akwai bukatar mahukuntan su sake duba tsarin aiwatar da kamen kayan da wa'adin aikinsu ya wuce. Ko a watan Agustan da ya gabata ma, mahukuntan birnin na Yamai sun kona ton 915 na kayan abinci da suka tashi daga aiki da magungunan jabu da miyagun kwayoyi da suka kama a kasuwanni da shaguna da wuraren shakatawa a cikin birnin.