Mai yiwuwa koriya ta arewa ta yi wasu ƙarin gwaje-gwajen nukiliya.
October 17, 2006Majiyoyi daga ƙasashen Amurka da Koriya ta kudu da Japan sun ruwaito cewa mai yiwuwa ne Koriya ta arewa na shirin sake yin wasu gwajin makaman nukiliya. Wani tabbataccen rahoto na cewa kumbon leƙen asiri na Amurka ya gano zurga zurgar mutane da manyan tankoki a kusa da inda Koriya ta arewan ta yi gwajin makamai a ranar 9 ga watan Oktoba. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice wadda a yau ta fara rangadin ƙasashe huɗu na yankin Asia a matakin diplomasiya domin neman ƙarin goyon bayan su wajen ƙarfafa ƙudirin Majalisar ɗinkin duniyar a kan koriya ta arewa, ta baiyana fatan koriya ta arewan ba zata aiwatar da gwajin nukiliyar ba. Da take jawabi ga manema labarai a washington Condoleezza Rice ta kuma yi gargaɗi da cewa takunkumin Majalisar ɗinkin duniya da aka sanyawa Koriya ta arewa ya isa ishara ga Iran a game da shirin ta na nukiliya. Ziyarar zata kai Condoleezza Rice zuwa ƙasashen Japan da koriya ta kudu da kuma China.