Mai yunkurin kai hari a Jamus ya kashe kansa
October 13, 2016Talla
Sebastian Gemkow, ministan shari'a daga jihar Saxony da ke a Gabashin Jamus ya ce zai bada karin bayani kan dalilan da ya sa wannan matashi mai shekaru 22 Jaber al-Bakr ya kashe kansa. Ministan ya ce zai yi jawabi a taron manema labarai da misalin karfe sha daya agogon Jamus tara agogon GMT a wannan rana ta Alhamis.
Wata majiya dai da ta tsegunta wa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA, ta ce an gano mutumin da aka tsare ya rataye kansa.
Al-Bakr wanda masu aikin bincike suka bayyana da cewa ya na da alaka da kungiyar nan ta IS an cafke shi a ranar Litinin bayan da aka dauki kwanaki biyu ana fafutikar neman inda ya boye, bayan da aka gano ababen fashewa da kayan hada su a dakin da yake zama a birnin Chemnitz.