Abincin zamani da na gargaji don gyara zaman aure
July 31, 2019Bisa lura da muhimmancin da abinci yake da shi musamman a zamantakewar ma'aurata wannan matashiya A'ishatu Musa Kida wacce ta yi karatunta na jami'a a fannin fasahar kiwon kifi, ta kashe makudan kudaden da take samu a sana'o'in da take yi wajen bude cibiyar koyar da girki na zamani da na gargajiya ga iyalai.
Yanzu haka daruruwan matan aure da 'yan mata har ma da zawarawa da matan da suka rasa mazajensu sun amfana da cibiyar da kuma aka yi imanin ta magance matsalolin aure da dama ba kawai a birnin Maiduguri ba har ma da wasu sassan jihar Borno.
Ko me yasa A'ishatu Musa Kida ta zabi bude wannan cibiya domin horar da mata yadda ake yin girki a wannan zamani?
"A matsayina na 'ya mace ba na jin dadin ana aibata mace a kan wani abin da bai kai ya kawo ba kamar girki. Komin son da miji yake wa matarsa, matukar ba ta iya girki ba, har yanzu akwai alamar tambaya tattare da zamantakewarki a cikin gida. Saboda haka muke koyar da mata ire-iren abincin da ya kamata su ba a mazajensu a kuma lokacin da ya dace."
Cibiyar koyar da girkin da ake kira Na'ish ta kuma samar wa mata da dama hanyar samun dogaro da kai inda wasu matan suka bude wuraren sayar da abinci.
A'ishatu Musa Kida ta ce yanzu haka sama da mata 500 ne suka samu horo a wannan cibiyar horar da abinci kuma da yawansu suna buga mata waya ko aike sakon kar ta kwana na yadda mazajensu suka yaba da sabbin dabarun zamani na girki da suka koya.
A wanann cibiyar dai za ka tarar da mata da 'yan mata suna bada himma wajen koyan girki dabam-dabam kama daga abincin gargajiya da na Bature har da kayan makulashe da ruwan zaki da ke hana maza fita daga gida.
Duk da abin da wannan baiwar Allah take samu bai taka kara ya karya ba a cewar ta in har ta gyara aure ta haifar da farin ciki a gidajen aure mata suka samu sana'a burinta ya cika.
A'ishatu Musa Kida ta ce ba ma san inda ta jefa takardun shaidar kammala karatun digiri ba kuma ma ba tada tsarin bayanai na mutum da ake kunshe a Curriculum Vitae wato ba saboda a cewar ta ba ta taba sha'awar aikin gwamnati ba.