1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maiduguri: Osinbajo ya kaddamar da rabon abinci

June 8, 2017

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya kaddamar da wani gagarumin shirin gwamnatin Najeriya na rabon kayan abinci ga miliyoyin 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da matsugun su.

Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a wani taron manema Labarai a Abuja.Hoto: picture-alliance/dpa

Duk da hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a birnin na Maiduguri a ranar Laraba da dare, Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya iso birnin na Maiduguri cikin tsauraran matakan tsaro domin kaddamar da abin da aka kira gagarurmin rabon kayan abinci ga 'yan gudun hijira da ke shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya. Wannan shiri wanda shi ne irin shi na farko da Gwamnatin ta kaddamar tun fara rikicin Boko Haram sama da shekaru bakwai, za a shafe tsawon kwanaki ana aiwatar da shi, inda za a raba ton na kayan abinci dubu talatin wanda zai lamushe kudi Naira miliyan dubu takwas. A cewar Osinbajo bayan namijin kokari da gwamnati ke yi na samar da zaman lafiya, yanzu kuma ta fito da wannan shiri wanda zai ba da damar raba abinci ga 'yan gudun hijira a zango-zango.

'yan gudun hijira na Arewa maso gabashin Najeriya.Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

'Yan gudin hijira a yankin jihar Borno
"Yayin da muka dawo da tsaro da zaman lafiya a shiyyar, mun ga akwai bukatar samar da kayyayin more rayuwa da ilimi da abinci da kulawar lafiya da matsugunnai da ma hanyoyin da za a sake tsugunar da al'ummar. Hakan ne ya sa muka kaddamar wannan shiri na samar da abinci domin 'yan gudun hijira. da wannan ne muke shaida wa 'yan uwanmu maza da mata da ke wannan shiyya ta Arewa maso gabashin Najeriya cewa kasar nan ta na sane da halin da suke ciki kuma ba mu rufe idanuwanmu ba kan haka."

Kayan abincin da za a raba wa 'yan gudun hijirar sun hada da shinkafa, dawar masara da waken Soya kuma dukkanin su ba wanda aka shigo da shi daga kasashen waje kamar yadda Mukaddashin Shugaban ya bayyana. Osinbajo ya kara da cewa nan da 'yan makonni, gwamnati za ta fito da wani sabon shiri na sake tsugunar da 'yan gudun hijirar da zummar ba su damar komawa gida don ci gaba da rayuwa:

'yan gudun hijira a Maiduguri da ke yankin Arewa maso gabashin Najeriya.Hoto: picture alliance/AP Photo

"Nan da makonni kadan za a kaddamar shirin kyautata rayuwar al'ummar da wannan rikici ya shafa domin karfafa kokarin da Sojojin su ka yi a wannan shiyya. A shirye muke mu ciyar da al'ummar mu gaba, mu taimaka musu su koma yankunan da ke da cikakken zaman lafiya domin su koma gonakin su don yin noma a daminar bana."

Gwomnan jihar Borno ya jinjina wa Gwamnatin Tarayya
Mukaddashin shugaban ya ziyarci fadar Shehun Borno da kuma sansanin 'yan gudun hijira na Bakasi, inda ya ga halin da 'yan gduj hijirar su ke ciki. Gwamnan jihar Borno Kashin Shetima ya yi godiya ga Gwamnatin Tarayya kan kokarin da ta yi a fannin yaki da 'yan kungiyar Boko Haram. A halin yanzu dai kura ta lafa kowa ya koma harkokin sa na yau da kullum, inda mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo da tawagarsa da suka hada wasu gwamnonin shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya su ka koma Abuja fadar gwamnatin Tarayya.

Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima.Hoto: DW/U. Shehu

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani