Brexit: May ta sha kaye a majalisar dokoki
March 13, 2019A kuri'ar da 'yan majalisar suka kada a ranar Talata, yan majali 391 sun ki amincewa da yarjejeniyar da Firaminista Theresa May ta gabatar yayin da 'yan majalisa 242 suka ce sun yarda.
Firaministar ta ce ta ji matukar takaici da matakin da 'yan majalisar suka dauka.
Sai dai da yake jawabi shugaban jam'iyyar adawa ta Labour Jeremy Corbyn yace ya kamata Theresa May ta sauya tunani kan kudirinta na neman ficewarBirtaniya daga kungiyar tarayyar Turai ba tare da cimma yarjejeniya mai ma'ana ba.
Yace gwamnati ta kuma shan kaye da gagarumin rinjaye. A yanzu wajibi ne su amince cewa shawarar su da yarjejeniyar da Firaminista ta gabatar basu sami amincewar wannan majalisar ba.
Firaminista Theresa May dai ta ce ta yi imani hanya mafi dacewa ita ce rabuwa cikin masalaha da karimci tsakanin Birtaniya da Kungiyar Tarayyar Turai.