Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kiran taimakawa Yemen da tallafin kudi
December 18, 2011Majalisar Ɗinkin Duniya ta buƙaci samarwa ƙasar Yemen mai fama da rikici, tallafin kuɗi na gudunmawar jin ƙai Dala miliyan 450 domin ceto ƙasar daga abin da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta kira faɗawa yanayi irin na Somalia. Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu ƙungiyoyin agaji dake aiki a Yemen sun faɗawa wani taro da aka gudanar a Dubai cewa ƙasar Yemen na buƙatar taimakon jin ƙai musamman a fannin abinci da harkar kula da lafiya da tsabtar muhalli da kuma samar da ruwan sha mai tsabta. Zanga zangar adawa da shugaban ƙasar mai barin gado Ali Abdalla Saleh da aka shafe kusan shekara guda ana yi ta durƙusar da tattalin arzikin ƙasar lamarin da ya raunana matsanancin halin rayuwar Jama'a tare da ƙarancin abinci da ruwan sha da kuma wutar lantarki. Wakilin hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya Unicef Geert Cappalaere ya ce idan ba'a yi wani abu cikin gaggawa ba, to kuwa nan ba da jimawa ba za'a fuskanci babbar matsala a ƙasar.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Usman Shehu Usman