Majalisar Ɗinkin Duniya za ta gudanar da bincike a Libiya
May 18, 2012Ƙwarrarun zasu fara gudanar da aikin bincikken domin tantance ko a kwai wasu sojojin haya na ƙasashen ƙetare da aka yin amfani da su a cikin yaƙin da aka gwabza a ƙasar.
Tawagar wacce zata fara ziyara a ranakun 21 zuwa 25 ga wannan wata bisa gayatar ƙasar ta Libiya, zata yi koƙarin haƙiƙance gaskiyar zarge zargen da aka sha yi akan wannan batu.Domin samar da hanyoyin magance matsalar, idan har hakan ya tabbata, kamar yadda shugabar tawagar Madame Faizal Pate ta baiyana.A cikin watan Satumba da ya gabata hukumar ta zargi sojojin hayar da ke mara wa tsoHuwar gwamnatin kanal Kaddafi bayada laifin keta hakin bil adama ta hanyar azabatar da jama'ar tare da karkashe wasu a birnin Tripoli.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman