1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Majalisar Amirka ta wanke Donald Trump

February 14, 2021

Majalisar dattawan Amirka ta wanke tsohon shugaban kasar Donald Trump daga zargin da aka yi masa da ya kai ga shirya tsige shi daga matsayinsa.

USA Ohio US-Präsident Donald Trump
Hoto: Reuters/J. Ernst

Tsohon Shugaba Donald Trump dai ya fuskanci zargi ne na tunzura magoya bayansa wadanda suka afka wa majalisar dattawan a ranar shida ga watan Janairu, a lokacin da ake tabbatar da zaben shugaban kasa mai ci, Joe Biden.

Santoci 57 ne da suka hada da 'yan jam'iyyar Republicans na tsohon shugaban bakwai suka kada kuri'ar amincewa, yayin da 43 suka nuna ki amincewa da hakan.

An dai gaza samun rinjaye ne da ake bukata wajen tsige Donald Trump wanda ya sauka daga mulkin kasar a ranar 20 ga watan jiya, inda bisa doka ake bukatar Sanatoci 67, wato biyu bisa ukun su ke nan.

Tuni ma dai tsohon Shugaba Trump ya yi godiya ga lauyoyin da suka tsaya masa, yana mai cewa ko ba komai, ya sake kafa tarihin tsallake wata kutungwilar.