1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Dunia ta gabatar da sakamakon bincike a kan rigingimmun kasar Togo

Yahouza sadissouSeptember 26, 2005

Yau ne Komitin Majalisar Dinkin Dunia, ya gabatar da rahoton binciken da ya gudanar, a game da ringinmun da su ka biwo bayan zaben shugaban kasar Togo, a watan Afrul da ya wuce.

Togo
TogoHoto: AP

Shugaban hukumar Majalisar Dinkin Dunia, mai kulla da kare hakokin bani adama, ya hada wannan komiti da a ka azza wa yaunin gudanar da bincike, domin gano zahirin gaskiya ,na yawan mutanen da su ka mutu, da wanda su ka jikkata ,da kuma wanda su ka bar gidajen su, a sakamaon wannan rigingimmu.

Shugaban komitin, da ya gudanar da binciken, Dudu Diene kakakin Majalisar Dinkin Dunia, a game da abun da ya shafi kabilanci, nuna wariya, da kyamar baki, ya ce a duk tsawon lokacin da su ka gudanar da wannan aiki, sun gane wa idan su abun al´ajabi.

A jimilce, mutane 400 zuwa 500 su ka rasa rayuka, a yayinda dubunnai, su ka ji mumunan raunuka.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar, ba ta bayyana sakamakon binciken da ta aiwatar ba, duk da cewa, ta girka komiti, da ta dorawa wannan yauni.

Saidai wata kungiya mai zaman kanta, da ke da goyan bayan gwamnatin, ta sannar cewa, mutane 58 ne, su ka mutu a yayin da su kuma yan adawa, su ka bada addadin mutane 811.

Sakamakon bincike na Majalisar Dinkin Dunia, yayi suka da kakkaussar halshe, ga gwamnatin kasar Togo, da jami´an tsaron wannan kasa, a game da abunda ya kira tozarci da ukuba, da su ka ganawa jama, mussman yan bangaren jam´iyun adawa.

Rahoton ya ce, kimanin sojojin 2.500, sanye da kayan farra hulla, su ka sade da mutane, inda su ka bada hadin kai, ga yan jam´iyar RPT mai mulki, dauke da sanduna, da kullake da wukake, da su ka yi anfani da su, domin hallaka magoya bayan jam´iyu adawa.

Wannan rahoto ya tabatar da cewa, baki daya ma zaben na shugaban kasar Togo, an gudanar da shi cikin yanayi mai hazo da magudi, ta hanyar kirkiro dokoki, cikin gaggawa wanda su ka tanadi samun nassara ga shugan Faure Yasimbe,da ya maye gurbin mahaifin sa Yasimbe Yadema.

A bangaren kashen ketare, rahoton ya bayyana cewa, yan assulin kasar Mali 8 su ka mutu, sannan da yan Niger 4.

A daya hannun kuma, rahoton ya zargi shuwagabanin adawa na kasar Togo, da rashin daukar matakan da su ka dace a lokacin da ya dace, domin kauce magoya bayan su, daga wannan kissan kiyasu.

A karshe rahoton ya gabatar da shawarwari, wanda inda aka bi su, zaman lahia zai tabbata a Togo.

Shawar farko ita ce, ta kaffa wani saban komiti, wanda zai hada kan yan kasa, domin komitin farko da shugaban kasa ya girka ba shi da goyan baya, daga wasu sassa na yan siyasa.

Sannan shawara ta 2, ta bukaci hukumomin Togo, su rusa dukkan kungiyoyin sa kai da su girka, da kuma gudanar da cikkakar kwaskwarima, ga rundunar tsaro ta kasa, sannan a karshe, bangarori daban daban na siyasa, yan adawa da masu rike da ragamar mulki, sun koma tebrin shawara, domin girka gwamnatin rikon kwarya da zata dukkufa, ga ayyukan ci gaban kasa.