Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa Njar taimako
August 20, 2010Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa ƙasar Nijar taimakon Dala Amurka biliyan 15 ƙwatakwacin sama da miliyar bakwai na kuɗin CFA domin yaƙi da matsalar yuwan da ta ke adabar ƙasar a sakamakon farin da ta ke fama da shi.
Maljalisar dai ta ce kusan miliyon bakwai na al'umar abinda ke zaman rabi ga yawan al'umar ƙasar baki ɗaya na cikin wanin hali na ƙarancin cimakka.
Sanan a tsakanin shekara ta 2009 dakuma wannan shekarar 2010 yawan yara ƙanƙana da ke kamuwa da tamowa ya ƙaru daga kashi 12 zuwa 16 inda a kowane sati yara kamar dubu shidda ne ake karɓa a cibiyoyin bada agaji na yaran.
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala