1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta soki lamirin kasashe masu hannu a rikicin Libiya

Mahmud Yaya Azare GAT
July 9, 2020

Babban Magatakardan MDD Antonio Guterres ya yi Allah-wadai da kasashen ketaren da ke sanya hannu a rikicin kasar Libiya, abin da ya bayyana a matsayin takaici ganin yadda ake kai makamai da kuma sojojin haya.

Libyen-Ägypten-Waffenruhe
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Yayin da yake jawabi gaban Kwamitin Sulhu wanda ya gudanar da taro na musamman kan rikicin na Libiya, ta hanyar bidiyon yanar gizo, Guterres ya bayyana damuwa kan yadda ake jibge sojoji kusa da birnin Sirte, wanda ke tsakiyar biranen Tripoli da Bengazi:


 "Lokaci na kure mana Libiya. Mun zura ido muna ganin yadda rikicin kasar ke daukar sabon salon da shi ne mafi muni a kasar. A  yanzu haka, duk da takunkumin hana sayar wa kasar makamai da kuma alkawarin da kasashen ketare suka dauka a taron Berlin na samar da yanayi mai kyau na sasanta rikicin kasar, kasashen ketare  dabam-dabam na ci gaba da rura wutar rikicin, ta hanyar ci gaba da kirge miyagun makamai a tsakiyar kasar da jibge tarun sojojin haya da ke gwabza fada."


 Shi ma shugaban Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kuma Ministan Harkokin Wajen Jamus,  Heiko Maas caccakar kasashen da ke katsalandan cikin rikicin na Libiya ya yi, yana mai nuna takaicinsa da yadda kasashen da ke da ruwa da tsaki wajen cimma yarjejeniyar dakatar da buda wuta da aka cimma a birnin  Berlin  na Jamus watanni shidan da suka gabata, sune kuma a yanzu haka suka tsunduma dumu-dumu wajen mayar da kasar ta Libiya filin daga:

Hoto: Getty Images/AFP/M. Kahana

"Katsalandam din da kasashen ketare ke yi shi ne babban alakakai a rikicin na Libiya. Abun ta da hankali ne a ce, a daidai lokacin da kasashen duniya suka rufe iyakokinsu, sai ga shi ana samun jiragen ruwa da na sama da motoci dauke da makamai da kuma sojin haya na kwarara cikin Libiya."

 Shi kuwa ministan harkokin wajen Rasha ,Lavrop, wanda sojojin hayar kasarsa da ke taya Haftar yaki a yanzu haka suke ci gaba da mamaye rijiyoyin man fetir din kasar ta Libiya, nuna irin kokarin da kasarsa ke yi don sasanta rikicin na Libiya ya yi:

Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

"Mun gamsar da rundunar sojin Libiya karkashin Janar Haftar har ta aminta da dakatar da buda wuta da shiga tattaunawar zaman lafiya, abun da ya rage, shi ne kasar Turkiya ,da ke goyan bayan gwamnatin hadin kan kasa, ta gamsar da Fayez Sarraj da shi ma ya zo ya bi sahu."

Masharhanta dai, irin su Bashir Abdulffattah na ganin cewa, matakin ko in kula da gwamnatin Libiya tare da hadin gwiwa da Turkiya ke wa wannan tayi na Rasha, babbar amsa ce kan dagewarsu ta amfani da karfin tuwo don murkushe abokan hamayyarsu:

"Ba na zatan Turkiya za ta aminta da tsagaita wuta.Tun da dama abun da ya kai ta Libiya yarjejeniyar soji ce, wacce ci gaba da yin aiki da ita tare da gwamnatin hadaka ne kadai zai kai ta ga cimma burinta na samun barrajewa da jibge sojojinta a Libiya."