MDD ta damu da hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza
October 20, 2025
A nan kuma Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta bayan tashin hankalin da ya sake barkewa mai nasaba da hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga dukkan bangarori da su mutunta daukacin alkawuran da suka dauka na yarjejeniyar tsagaita wuta, in ji kakakin sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Stéphane Dujarric.
Karin bayani: Isra'ila ta ce ta dakatar da kai hare-hare a Gaza
Hare-haren da Isra'ila ta kai a yankin Falasdinu sun yi silar mutuwar akalla Falasdinawa 45 a ranar a jiya Lahadi, kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta yankin Gaza ta sanar, lamarin da ke barazana ga zaman lafiya da aka cimma atsakanin bangarorin biyu karkashin shawarwarin shugaban Amurka Donald Trump a ranar 10 ga wannan wata