Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da gayyatar kai ziyara sansanin Guantanamo
October 29, 2005Talla
MDD ta tabbatar da gayyatar da Amirka ta yiwa wasu ´yan kare hakkin bil Adama masu zaman kansu zuwa sansaninta na Guantanamo inda ta ke tsare da mutanen da ta ke zargi da aikata ta´addanci. Kakakin hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD dake birnin Geneva Jose Diaz ya tabbatar da wannan gayyata wadda ta zo shekaru 4 bayan da MDD ta fara neman izinin gudanar da bincike a kurkukun, inda ake zargin sojan Amirka da cin zarafin firsinoni. A halin da ake ciki firsinoni kimanin 24 ke yajin cin abinci a sansanin na Guatanamo. Kakakin ya ce a ranar litinin mai zuwa jami´ai 3 na MDD zasu ba da sanarwa game da ranar da zasu kai ziyarar ta ganewa ido a sansanin na Guatanamo dake kasar Cuba.