1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da rikicin Sudan

April 25, 2012

Yayin da rikicin Sudan da Sudan ta Kudu ke ci-gaba da tabarbarewa Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen biyu su nuna halin dattako.

A SPLA soldier walks in a market destroyed in an air strike by the Sudanese air force in Rubkona near Bentiu April 23, 2012. Sudanese warplanes carried out air strikes on South Sudan on Monday, killing three people near the southern oil town of Bentiu, residents and military officials said, three days after South Sudan pulled out of a disputed oil field. REUTERS/Goran Tomasevic (SOUTH SUDAN - Tags: CIVIL UNREST POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya umarci kasar Sudan ba tare da jinkiri ba ta dakatar da farmakin da take kaiwa ta sama akan Sudan ta Kudu a takaddamar dake wakana tsakanin kasashen biyu game da yanki mai arzikin mai dake kan iyakarsu. Manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniyar sun tabbatar da cewa an kashe akalla mutane 16 tare da jikata wasu 34 a farmakin jiragen saman a Sudan ta Kudu. Kwamitin sulhun mai wakilai goma sha biyar ya sake yin sabon kiran tsagaita wuta, yana mai gargadi da cewa zai yi nazarin daukar wasu matakai nan da kwanaki masu zuwa domin kawo karshen arangama a tsakanin kasashen biyu na gabashin Afirka makobtan juna. A yayin wata ziyara da ya kai kasar Sin, shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya zargi kasar Sudan da baiyana kaddamar da yaki akan kasarsa. A hannu guda dai sojojin Sudan sun musanta kai farmaki da jiragen sama. Rikicin baya bayan nan dai shine mafi muni tun bayan da Sudan ta Kudu ta sami mulkin kai.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe