1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yawan ta'adin zafi

July 26, 2024

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi gargadi a kan tsananin yanayi na zafi da al'umar duniya ke fuskanta sakamakon matsaloli na sauyin yanayi.

Yadda ake fama da tsananin zafi a nahiyar Turai
Yadda ake fama da tsananin zafi a nahiyar TuraiHoto: Nikolas Kokovlis/NurPhoto/Imago Images

Wannan gargadi na Antonio Guterres ya zo ne bayan bayyana ranar Litinin da ta gabata a matsayin ranar da ta fi kowacce zafi a tarihi.

Zafin dai a cewar masana ya fi haddasa kisa sama da sauran bala'o'i da sauyin yanayi ke haddasawa, masalan guguwa ko kuma ambaliyar ruwa.

Zafin da ke kisan mummuke, ya yi sanadin mutuwar akalla mutum dubu 489 duk shekara a tsakanin shekara ta 2000 zuwa 2019.

Yayin kuma da guguwa ke kashe rayuka kimanin dubu 16 a kowace shekara a duniya.

Don haka ne ma Majalisar Dinkin Duniya ke kiran da a kara azama wajen rage barnar da zafin ke yi, ta hanyar ankararwa da kuma daukar matakai na sanyaya yanayi gami da kyautata tsara birane da kuma kare masu aiki a filin Allah Ta'ala.