1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da hare-hare a Siriya

May 3, 2025

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir kan jerin manyan hare-hare da Isra'ila a Syria, hare-haren kuma da Isra'ilar ke fadin tana yin su ne da nufin kare 'yan kabilar Druze marasa rinjaye.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio GuterresHoto: Bianca Otero/ZUMA Press Wire/picture alliance

Tun da yammacin ranar Juma'a ne dai aka fara ganin wasu munanan hare-hare a wasu sassan birnin Damascus da ma wasu yankuna na kudanci da tsakiyar kasar ta Syria.

Sabbin hare-haren ranar Asabar kuma sun zo ne sa'o'i kalilan bayan wani da mayakan saman Isra'ila suka kai kusa da fadar shugaban kasar Syria, bayan gargadin a guje wa yankunan da 'yan kabilar Druze din ke a ciki.

Wani rikicin kwanaki uku tsakanin masu goyon bayan gwamnatin Syria da 'yan kabilar Druze da ke rike da makamai, ya ji sanadiyyar mutuwar akalla mutum 100.