1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Isra'ila akan Falasdinawa

Zulaiha Abubakar
April 27, 2018

Babban kwamishinan kare 'yancin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein ya ja hankalin kasar Isra'ila kan ta guji amfani da karfin jami'an tsaro a kan falasdinawan da ke gudanar da zanga-zanga.

Gaza
GazaHoto: Reuters/I.A. Mustafa

Kwamishinan yayi wannan kira ne kafin Falasdinawan su fara zanga-zangar kashi na biyar a yau Juma'a a wani yunkuri na karya shingen da aka yi wa yankin su,ya kuma kara da cewar Isra'ila tayi watsi da gargadin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi mata bayan da ta yi amfani da makami mai guba akan fararen hula lamarin da yayi sanadiyyar rasa rayukan Falasdinawa 35 tare da jikkata sama  da 1500 .