1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Makomar sulhun Hamas da Isra'ila a MDD

Abdoulaye Mamane Amadou
November 17, 2025

Majalisar Dinkin Duniya za ta kada kuri'ar shata makomar Gaza, makwanni bayan da yarjejeniyar sulhu tsakanin Hamas da Isra'ila ta fara aiki.

Taron MDD
Taron MDDHoto: BPMI Setpres

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, zai kada kuri’a kan sabon daftarin shirin zaman lafiya da shugaban Amurka Donald Trump, ya gabatar wa bangarorin Hamas da Isra'ila.

Isra'ila ta ce ita za ta zabi sojojin ketare don tsaron Gaza

Wannan matakin na zuwa ne bayan matsin lambar da Amurka ta yi, tare da yi hannunka mai sanda kan fargabar sake barkewar rikici, idan har ba akai gaza tabbatar da wani tsari mai dorewa a yankin Gaza, bayan da aka cimma yarjejeniyar sulhu tsakanin Hamas da Isra'ila a ranar 10 ga watan Oktoba.

Firaministan Isra'ila ya ba da umarnin kai hare-hare Gaza

Wata majiya ta tabbatar wa manema labarai ciki har da AFP cewa, kudurorin dake da muhimmanci a sabon daftarin sun kunshi girke sojojin kasa da kasa domin tabbatar da tsaron Gaza da za ta taimaka wajen tabbatar da tsaron yankin da batun tsare iyakokin Gaza da Isra'ila da Masar.

Hamas za ta mika gawar wani sojan Isra'ila

Kazalika shirin ya tanadi a rage karfin ikon Hamas da kwace makaman soji a hannun daukacin kungiyoyin da ba na gwamnati ba, sannan daftarin ya tanadi kafa gwamnatin wucin gadi a yankin har zuwa ranar 31 ga watan Disamban shekarar 2027.